Take a fresh look at your lifestyle.

Sojojin Sudan Sun Kame Birnin A Kudancin Kordofan

21

Dakarun Sojin Sudan (SAF) sun sanar da cewa sun kwace iko da birnin Al-Dibaibat mai matukar muhimmanci a jihar Kordofan ta Kudu bayan fafatawa da dakarun da ake kira Paramilitary Rapid Support Forces (RSF).

Kakakin SAF Nabil Abdalla ya ce a cikin wata sanarwa da ya fitar  “Rundunar sojin sun yi nasarar fatattakar Al-Dibaibat.”

Sojojin Sudan sun yada bidiyo a shafukan sada zumunta daga cikin Al-Dibaibat, suna sanar da rashin nasarar RSF.

Har yanzu dai RSF ba ta ce uffan ba game da sanarwar da sojojin suka yi na iko da birnin.

Al-Dibaibat ya mallaki dabarun soja da muhimmanci yayin da yake zaune a wata babbar hanyar da ta hada jihohin Kordofan uku. Hanya daya ta bi ta kudu zuwa Dilling da Kadugli a jihar Kordofan ta Kudu wata kuma ta wuce yamma zuwa Abu Zabad da Al-Fula a jihar Kordofan ta Yamma  sai kuma hanya ta uku ta hanyar El Obeid  babban birnin jihar Kordofan ta Arewa.

‘Yan tar da birnin na zuwa ne kwanaki kadan bayan da sojojin Sudan suka sanar da cewa za su ci gaba da mamaye jihohin Khartoum da White Nile.

Tun a watan Maris sojojin Sudan ke fadada yankunan da suke iko da su yayin da RSF ke ci gaba da ja da baya.

Sudan ta fada cikin mummunan rikici tsakanin SAF da RSF tun watan Afrilun 2023.

Yakin dai ya yi sanadin mutuwar dubun dubatar mutane tare da tilasta wa miliyoyin mutane barin gidajensu a cikin kasar Sudan da kuma kan iyakokin kasar.

Xinhua/Aisha.Yahay, Lagos

Comments are closed.